BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Tambayoyi da amsarsu tare da
Mallam Ibrahim Zakzaky na ashirin da bakwai
Ko ya halatta musulmi ya kada kuri'a ko a kidaya shi?
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Muna so a yi mana bayani kan halascin kukan mutuwa. Haramun ne ko kuwa halas ne?
Daga Nura Mu'azu Kano 0802 469 6903
SHAIKH ZAKZAKY: To lalle halas ne a yi kukan mutuwa. Abin da aka hana shi ne ihu da kururuwa da kiran wailu, da cewa an mutu an lalace, da an yi hasara, da irin wadannan. Da tsattasaga riguna, da ciccisge gashi, da diban kura a watsa a jiki. To duk irin wadannan ne aka hana. Amma ba kuka na sharbe da hawaye ba, wanda lazim zuciya in ta koka babu yadda za a yi a gintse wa ido yin wannan. Amma an hana abin da na ambata na kururuwa da ihu da kiran wailu; sune haramun.
TAMBAYA: Malam menene hukuncin wanda ya zagi Malaminsa?
Daga Kabiru A. Jalingo 0802 744 5126
SHAIKH ZAKZAKY: To zagin Mumini haramun ne, yakar sa kuma kafirci ne kamar yadda ya zo a hadisai. Saboda haka ya aikata haramun.
TAMBAYA: Malam menene hukuncin Shugaba mayaudari?
Daga Kabiru A. Jalingo 0802 744 5126
SHAIKH ZAKZAKY: Yaudara haramun ce. Daga Shugaba ma za ta fi tsanani tunda shi ba yana yaudarar mutum guda bane, kila yana yaudarar mutane ne masu yawa.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ko ya halatta musulmi ya kada kuri'a, ko kuma ya bari a kidaya shi a kidayar da za a yi nan gaba a Nijeriya?
Daga Hafsa Aliyu Kaduna, Karamar Hukumar Takai a jihar Kano 0803 944 6322
SHAIKH ZAKZAKY: To in dai halasci ne ya halatta, sai dai a wadansu 'zuruf' din yana iya zama…, musamman kamar shi dai na kidaya ba wani ishkali dangane da shi, cewa a kidaya ka, wannan ba ta inda ya haramta. Amma kada kuri'a shi wannan akwai ishkal a ciki, saboda yana iya yiwuwa ya zama maka wajibi, yana iya zama ya zama maka mustahabbi, yana iya zama maka haramun, yana iya zama ma in ka kada, ka yaki addini ne. Ya danganta da wa ka jefa wa kuri'ar ne?
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam mutum ne yake aikin tuka wani mutum wanda ba Musulmi ba, wani lokacin yana tsayawa ya tare karuwa, ko kuma ya sayi giya? Malam ya mutum zai yi kenan?
Daga 0802 704 3450
SHAIKH ZAKZAKY: To lalle in ya taimaka masa ga wani aiki na laifi, to shi ma ya yi laifi. Saboda haka idan tukin nasa zai taimake shi ga aikata mummunan aiki, to lalle bai halasta masa ba. Sai ya nemi tuka wani, ko kuma ya gindaya masa sharadin cewa shi zai tuka shi ne kawai a abin da ya halasta a addininsa. Kamar ya kai shi wurin aiki, ko wuraren da ya halatta a shari'a, ya iya kai shi, in kuma bai yarda ba shi kenan sai ya nemi wani aikin, tunda ba lalle ne ya tuka wannan mutumin ba. Ala'ayyi halin dai, wato tuka shi ya zuwa muhallin aikata laifi, shi ma laifi ne.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ina hukunci mutumin da yake aiki a waje mai nisa, amma yana da mata biyu sai ya dauki daya ya je da ita?
Daga 0802 704 3450
SHAIKH ZAKZAKY: To wala'alla shi yana tambaya dangane da sallar kasaru ne da batun shan azumi, kodayake bai ambata ba. Idan ya yi haka nan ya zama mai gida biyu kenan. Duk inda ya je yana gida ne. Amma in a tsakani nisan ya kai 'masafa' na kasaru, to in salla ta same shi a kan hanya zai yi kasaru ne, amma in ya je can (kowanne) inda ya ajiye matar tasa, ya zama gida.
TAMBAYA: To amma idan ya kasance ya ajiye mata daya a wani gari, dayar kuma tana a inda yake aiki, yakan yi kwana biyar a nan, a can kuma in ya je kwana biyu kawai yakan yi. To ina matsayin wannan?
SHAIKH ZAKZAKY: Ala'ayyi halin, da ma shi dai rabo. Akwai rabon kwana a tsakanin ma'aura, na ma'aura biyu. Saboda haka kasantuwar ya ajiye wannan, ya ajiye wannan, bai kawar da hakkin rabo ba, duk inda yake sai ya raba su. In suna tare, rabon kwana na nan. In kuma yana iya yiwuwa ya je nan ya je nan, to duk sai ya raba kwanan. Ba shi da hujjar cewa in waccan tana can zai kwana biyar, wannan kuma ya kwana biyu, ya rika yin Weekend. Sai dai in ita ma dayar ce ta yarda, ta yarda da karshen mako kawai, kwana biyu, sauran biyar din ta ba dayar. Sai dai in haka nan ne, in ba haka ba, rabon kwana dai zai zama masa tilas. Saboda haka, ko yana aikin ne, sai ya je gidan da wadda kwananta ne yake.
TAMBAYA: Akramakallah. A wajen yin maganin wasu cuttukan ana yin amfani da barasa da naman alade. Shin yana halatta a da'irar fikihun Musulunci a yi 'prescribing' ga wanda ba Musulmi ba?
Daga Abdulkarim Ramalan Fauziyya Medical and allied services Rigasa Kaduna
SHAIKH ZAKZAKY: To lalle shi wanda yake musulmi ai ba ya ta'ammuli da giya da naman alade ballantana har ya yi wa wanda yake ba musulmi ba Prescription din. Saboda ko da shi wanda yake ba musulmi ba, shi a wurinsa halas ne, amma kai a wurinka ai ba halas ne ka yi ta'ammuli da shi ba. Ba abin da ya hada ka da shi ballantana har wani ya zo wajenka ba shi da lafiya ka ce, to ka ci naman alade, ko kuwa ya sha giya ne, masalan. Tunda kai a wurinka ka san wadannan najasu ne ba ka da wani tu'ammuli da su. Saboda haka kai babu abin da ya hada ka da su. Amma in har ka ce masa ya sha giya, ko ya ci naman alade, ko kuma ya sha wani magani mai giya, ko kuma mai naman alade, kamar ka umurce shi da ya ci, ya sha wadannan abubuwan kenan, kai kuma babu abin da ya hada ka da su.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ko ya halatta dan kasuwa ya sayi kayan da Hukumar Kwaston ta kwace daga hannun mutane bisa zargin sun karya dokar kasa, kuma aka yi gwanjonsu?
Daga Aminu Layin Sarki Abuja 0805 798 7502
SHAIKH ZAKZAKY: To ya danganta da yadda al'umma ta fahimci abin ne. Idan an fahimci cewa zalunci aka yi, kamar wato an kwace kayan mutane ne bisa zalunci, to, idan kai ka saya, kai ma ka taimaki azzalumai kenan ga zaluncinsu. Amma idan da ma wani abu ne da ake ganin da ma haka doka take bisa ka'ida, in an karbi wadannan karikitai akan yi gwanjonsu ne ga duk mai bukata ya saya tunda sun koma na Hukuma, to shi kenan a nan sai ya zama babu laifi.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ko yana halatta mace ta yi limancin salla?
Daga Sani Adamu Bajoga Funa-kaye jihar Gombe
SHAIKH ZAKZAKY: …..Sai dai magana maras karfi na cewa yana iya yiwuwa, ya halasta mata ta yi wa 'yan uwanta mata. Har wasu na cewa idan har za ta yi din, to ba za ta wuce gabansu ba, za ta zama a cikin sahun farko nasu a yayin da take masu limancin, in su zallarsu mata ne. Amma ko shi ma wannan ba wata magana ce da 'kada'an' aka yanke a kai ba. Amma ta yi wa maza da mata, wannan da ma ba zai yiwu ba.
TAMBAYA: Asslamu alaikum. Malam don Allah ina hukuncin 'games' na wayar GSM da ake yi. Haram ne ko halas?
Daga Ibrahim Abubakar Pombeguwa jihar Kaduna 0803 972 7211
SHAIKH ZAKZAKY: To wannan bai bambamta da sauran wasanni ba. Wanda yake hukuncinsu kamar sauran wasanni ne, in za su shagaltar da kai ga barin salla da zikir, suna iya haramta. In kuma suna kara maka ilimi da basira da fid da matsaloli, da wasa kwakwalwarka, suna iya halatta. Ko su ma kar ka cika yawan yin su, kar ka cika shagalta da su sai a yayin da kake ganin za su amfane ka.
TAMBAYA: Akramakallah. Na ba da bashi, amma da iznin mai kayan na bayar, amma kuma sai wanda aka ba bashin ya ki biya. Ni da nake tsakiya ya zan yi kenan?
Daga Khalid Rijiyar Lemo Kano 0802 881 0135
SHAIKH ZAKZAKY: To tunda da izinin mai kayan ne, wannan ai ya zama sassauka, ka ga shi mai kayan ne yake bin bashin ba kai ba, tunda kai sa ka aka yi ka bayar da bashin. Saboda haka idan ta hanyarka ne kawai za a karbo, yadda ka shiga tsakiya din wajen bayarwa, haka za ka shiga tsakiya din wajen karbowa. In kuma bai zama lazim ba, shi sai ya koma kan shi mai kayan, tunda shi ya ba da izini, shi zai karbi abinsa. Bai zama matsalarka ba ala'ayyu halin, tunda da izini ka yi.
TAMBAYA: Malam menene ya sa duk surori a cikin Alkur'ani suna farawa da bismilla, amma ita suratul Tauba ba ta da shi.
Daga Ibrahim Sabo 0803 207 672
SHAIKH ZAKZAKY: Dalili shi ne haka nan kawai aka ruwaito, illa iyaka. Allah kuma kadai ya bar wa kansa sanin hikimar da ke ciki.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Allah ya gafarta Malam, shin ya halatta dan Ja'afariya ya ja wanda ba dan Ja'afariyya ba salla?
Daga Abdullahi Aliyu Jambutu Wourd Jimeta Yola jihar Adamawa. nene2005@yahoo.com
SHAIKH ZAKZAKY: Sanannen abu ne cewa dukkan mazahib sun inganta yin salla a bayan ma'abocin wata mazhaba din. Lasiman dai Imamiyya, sun yarda cewa ya halatta ka yi salla a bayan ma'abocin wata mazhaba. Wannan ma ka yi salla kenan, ballantana kuma idan kai ne Liman, ai ka ga bai ma shafi sallarka ba sam-sam. Inda ma mishkila takan taso shi ne, in akwai bambamci tsakanin yadda hukunce-hukuncen sallarka yake da yadda na Limamin da kake bi yake. Ta yadda yana iya yin wani abin da kai a wurinka ma salla ta baci, amma duk da haka aka ce ya inganta ka bi shi salla din. To ballantana in kai ne Liman, ai ba wata mishkila sam-sam.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ina matsayin dan uwan da bai son zuwa makaranta, duk da kuwa bai yi karatu ba tun a baya?
Daga Yunusa Yakubu Abuja 0805 375 0839
SHAIKH ZAKZAKY: To wajibinsa ne dai ya yi karatu. Saboda haka karatu in ya zama tilas ba za a same shi ba sai an je makaranta, sai ya je makaranta din. Kuma tunda karatu ne kawai ya ce bai yi ba, bai fadi wane karatu bane? Za mu kaddara cewa na wajiban ayyukan addini dinsa ne ya zama masa wajibi. Saboda haka wajibinsa ne ya bidi wannan ilimin, amma ba wai zuwa makaranta ne ya zama wajibi ba. Domin karatu ana iya yin sa ba tare da an je makaranta ba, ko da a gidansu ne in yana iya samun karatun. Amma dai abin da ya zama wajibinsa ya yi ibada, ya zama wajibinsa ya san yadda ake yin sa. In kuma ba zai samu ilimin ba, sai ya tashi ya je wani wuri, to zuwa wannan wurin sai shi ma ya zama wajibi.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam dangane da istahara akwai ta kuwa a Imamiyya? In akwai ta muna neman karin bayani daga wajen Malam.
Daga Muhammad Sani Beni Nijeriya 0802 704 3450
SHAIKH ZAKZAKY: Eh akwai istihara, kuma in ya duba cikin ma'athurat zai ga sigoginsu daban-daban. Mafi kyawun istihara shi ne wanda mutum ya yi sallar raka'a biyu da daddare ya karanta addu'a ma'athuri yana neman Allah (T) ya zaba masa abin da ya fi alheri. Ba ya nemi ya tara sanin cewa menene zai faru ba, ya roki Allah dai in alheri ne ya sa ya yi, in kuma sharri ne ya kautar da shi ga barinsa. To duk wanda ya ga ya yiwu, to sai ya ga zabin Allah ne kenan. Wannan shi ne. Amma akwai shi da yawa a cikin ma'athurat.
TAMBAYA: Allah ya fagarta Malam, wani ne ya kira wani dan uwa musulmi ta tarho, da ya amsa masa, maimakon ya yi sallama, sai ya ce, "Ya Allah." Ya matsayin hakan a Musulunci?
Daga Muhammad Abubakar Alaba Internatiolan Market Legas 0803 330 6456
SHAIKH ZAKZAKY: To tunda "Ya Allah" ya ce, sai shi kuma ya ce masa Assalamu alaikum, tun da dai ba an ce ba a cewa Allah bane. An san dai in ana magana ana sallama ne, in wani bai maka sallama ba, kai sai ka yi masa. Ko da da ya buga, ba "ya Allah" ya ce ba, ya ce maka hello ne, ko sannu, ko ina kwana? Sai ka ce lafiya lau, assalamu alaikum. To ba shi kenan ba? Ko assalamu alaikum wa rahmatullah lafiya lau. An ce mafi alhairinku shi ne wanda ya fara sallama. Saboda haka idan mutum bai yi maka sallama ba, kai sai ka yi masa.
TAMBAYA: Malam mutum ne ake ba shi ajiyar kudi yana ajiyewa a ma'ajiyarsa (Akawunt na banki), shi ba shi da ko kwabo a ciki, ko zai iya karbar ruwan da ake badawa?
Daga Muhammad H. Power
SHAIKH ZAKZAKY: To idan an ba shi ajiyar kudi, ya samu ya dauka bashi a kashin kansa ya yi amfani da shi matsawar duk lokacin da mutumin ya zo bidar kudinsa, kudin nasa zai ba shi. Amma idan ya yi ciniki wanda ya karu, to lallai kudin na wanda ya ba shi ajiya ne.